Bam ya tarwatsa wata yarinya, wadda ake kyautata zaton ‘yar kunar bakin wake ce, ‘yar kimanin shekaru 14 da haihuwa wadda wasu mutane biyu ke wa jagora daura da Masallacin Jumma’a na Aliyu Ibn Abu-Dalib da ke daf da shatale-talen Dangi na kan Titin Zariya, wanda kuma ke makwabtaka da unguwar Gyadi-gaydi a birnin Kano da misalin karfe tara da kwata na dare a daidai lokacin da ake kammala Sallar Tarawihi a masallacin mai cike da jama’a.
Wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya ce mutanen sun sauke yarinyar ne daga wata mota a bakin titi sannan su ka amurce ta ta shiga harabar masallacin. Mahmud Kwari ya ruwaito wani ganau na cewa daya daga cikin mutanen da yarinyar sun doshi masallacin har sun tsallaka shatale-talen sai bam din ya fashe; ya yi kaca-kaca da ita. Amma mai tafiya da itan ya lallaba ya tsere. To sai dai da alamar wasu mutane biyu sun samu munanan raunuka ko kuma sun mutu.
Ganau na biyu kuma ya ce fashewar bam din ke da wuya sai aka rufe masallacin saboda a kare mutane. Ganau din, wanda aka sakaya sunansa y ace jami’an tsaron da ke daura da wurin ma sun yi ta harbe-harbe bayan tashin bam din. To saidai ya ce ga dukkan alamau dai babu wanda ya rasa ransa. Rundunar ‘yansandan Kano ta tabbatar da mutuwar yarinyar da kuma ranin da wasu mutane biyu su ka ji.
Your browser doesn’t support HTML5