Aljannar Mata na Samuwa a Watan Azumi

Mata

A watan Azumi watan ibada da kyautatawa ga iyalai dama sauran al’umah, matan kan fuskanci wasu abubuwa da kan sasu cikin tsaka mai wuya, musamman ma idan akece mace tana aikin gwamnati ko na kanfanoni masu zaman kansu, kana kuma ga aikin idabada na gidan miji.

Wata baiwar Allah, data bayyanar da irin wasu kalubale da takan fuskanta a cikin wannan watan, da kuma nuni da cewar wadannan matsalolin kusan yana kan mafi akasarin mata baki daya ne, masu aiki da marasa aiki. Domin kuwa yakamata ace masu gidaje su dinga tausayama matansu, a irin wannan yananyin, mafi akasarin wadannan matan suna aiki ne don bada tasu gudunmawa ga iyalan su, shiyasa suke aiki kana ga aikin cikin gida na iyalai, ashe kuwa wannan wani lokaci ne da yakamata masu gidaje su dukufa wajen yima iyalansu addu’a dagode musu da dauwainiya.

Domin kuwa a lokutta da dama, idan akace mace taje aiki ta kuma dawo, sai kuma ta fara shirye shiryen aikin kayan budabaki, don ganin ta kyautata ma mijinta, to a karshe dai za’aga cewar mace bata da wani lokaci na hutawa, don burinta shine ta kyautatama kowa, wajen aiki ma suna so suga tayi aikinta yadda yakamata batare da samun wata tangardaba.

A irin wannan yanayi akwai bukatar masu gidaje, sudinga bada tasu gudunmawa a wannan yanayi da ake ciki, don ta haka ne kawai matan suma zasu samu karfin gwiwar kyatatawa ga mazajensu. Su kuwa mata suji tsoron Allah, suyi amfani da wannan wata wajen farantama mazajensu rai dama daukacin iyalansu baki daya, domin samun falalar wannan watan.