A jiya Lahadi, an gudanar da wani taro a babban birnin jihar Kaduna, mai take Kalubalen da Musulunci ke fuskanta a wannan karnin. A wajen wannan taron dai Mai-martaba Sarkin Kano, Malam Sanusi Lamido Sanusi lll, ya gabatar da bukatar da akeda ita a kan gwamnatoci, dangane da samo hanyoyin magance wadannan matsalolin cikin gaggawa, musaman ma ga matasa. Kasancewar kungiyoyin ta’addanci nayi amfani da wadannan matasan wajen tada zaune tsaye.
Musamman ma, wadannan matasan akanyi amfani da kafofin yanar gizo, wajen chanza musu tunaninsu da karkatar da irin akidarsu. Sukuwa wasu ma suna ganin ai haryanzu ba'a kai matakin da za’a iya wankema wadannan matasan kwakwalwa ba wajen shiga irin wadannan kungiyoyin ba, don kuwa suna gani cewar irin wannan cigaban bai kawo kasashen su masu tasowaba.
A bangare daya kuma, wasu na ganin cewar idan har ba a samo wasu hanyoyi da za’a dinga bayyanar ma al’uma da irin wadannan kungiyoyi masu muanana manufofiba, to lallai za’a iyashiga cikin wasu munanan halaye a nan gaba kadan. Domin kuwa wadannan kungiyoyin kanyi amfani da matasa, wajen nunamusu cewar gwamnatoci na tauye musu hakokinsu a kowane mataki, don haka yakamata su tashi tsaye wajen yakar wadannan gwamnatocin, tunda wannan yanar gizon ana iya amfani da ita a fadin duniya da wasu a ko’ina su samun dammar kaiwa ga wadannan matasan.
Shikuwa wani masani a harkar sadarwar matasa, Malan. Nura Iro Ma’aji, yana ganin cewar yakamata gwamnatoci, su tashi tsaye haikan wajen, samar da wasu hanyoyi na yanar gizo da za’a dinga bayyanar da munanan ayyukan wadannan kungiyoyi, ga matasa dama duniya baki daya. Domin su fahimci cewar wannan kafofin yanar gizon, kamata yayi suyi amfani dasu ta yadda ya dace, da ciyar da kasa gaba, kana da kara fahimta ga al’umah ba aikin ta'addanci ba.