Tushen Gaskiya Daga Makaranta Ake Samoshi

ilimi

Daya cikin dubbai, a babban birnin da yafi kowannen girma a duniya, wato New York, an samu wasu yara fiya (5) da suka fadi jarabarwar kamala karatun sakandire. Wannan yasa an daga adadin makin da ake bukata kowane yaro ya samu a jarabarwar karrshe, zuwa maki 65. Kwatan kwacin kiredit 10.

A cewar wata marubuciyar New York post, Susan Edlman, ana zargin wata makarantar sakandiren koyar da gyaran mota, a karamar hukumar Greenpoint, da karama wani dalibi maki, a darussanshi guda biyu, don yasamu ya shiga ajin gaba, duk dai da cewar wannan dalibin ya fadi darasin Bayaloji, da lissafi. A nashi ganin dai, wannan dalibin yana gani cewar yayi iya kokarinsa don haka ya chan-chanci a kara mishi wannan makin.