Shan Kwaya ga Matasa na Haddasar da Hauka

Kwaya

Malama Amina Garba Gumel, shugaban kungiyar mata ta YINFOBA, kungiya mai yaki da shaye shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, tayi muna karin haske dangane da yunkurin kungiyarsu, wajen ceto matasa maza da mata masu shaye-shaye.

A baki daya kunkiyar su ta samu dammar shawo kan matasa fiyeda daribiyu, wadanda sukasa kansu cikin shaye shaye, sukanyi iya kokarinsu wajen ganin sun ankarar da mashayannan, ilolin wadannan shaye shayen da ma irin abubuwan da sukan iya haifarwa. Sukan lurar dasu dangane da wasu kadan daga cikin ilolin yin hakan, ga mata sukan iya samu matsalar da zata hanasu haihuwa, ko su haifi yara da wasu nakasa.

Sukuwa matasa wannan shaye shayen kan haddasar musu da hankali (Hauka) rashin da’a tarbiyya, dama rashin kunyya, da ma dai makamantan hakan. Ta kara dacewar wannan kungiyar tasu mai zaman kantane, basa samun tallafi daga gurin kowa, dan kuwa sun rubutama gwamnatoci da neman agaji, amma har yanzu babu wani labari, don haka suna kara kira da babbar murya da mahukunta, da masu hannu da shuni su bada himma wajen taimakama kungiyoyi masu yunkuri yaki da shaye shaye, don a samu a rage yawan shan barasa da kwayoyi a tsakanin matasa.