Samari sun fara gudun 'yan matan su a saboda fargabar kayan shan ruwa da na Sallah.
Kowace kabila ko kasa nada yadda suke gudanar da al’adunsu daban-daban, a kuma lokutta iri-iri. A kasar Hausa akwai wata dadaddiyar al’ada, wadda matasa kanyi wa ‘yanmatan da suke nema hidima, don kyautatawa a wasu lokutta a cikin shekara. Samari sukanyi ma ‘yan matansu hididdumu kamar nayin dinkin kaya, kayan azumi, kamarsu madara, kayan abinci, sayan wasu kayan kwalliya da dai makamantansu, wanda ta hakane soyayay ke karuwa a tsakanin masoyan biyu.
A tabakin wasu matasa a bana abun ya chanza, wanda suka bayyanar da wadansu dalilai da suke ganin su ne suka canza lamarin. Matasan dai naganin cewar mafi akasarin ‘yan matanan ba wai da gaske suke ba, don kuwa kana iya ganin mace da samari fiye da daya, samari kanyi iya bakin kokarinsu suga cewar sun kyautata ma wadda suke so, amma su kuwa wannan matan tunaninsu wanene zai kawo musu kaya masu yawa, ba wai tana sonshi tsakani da Allah bane, don haka yasa samari suna ganin dasu kashe ma irin wadannan matan kudadensu to gara su yima ‘yan uwansu hidima.
Wasu ma naganin cewar mafi akasirin wasu mazan na guduwa su bar ‘yanmata a wasu lokutta, musamman lokacin azumi, maulidi, domin kuwa a irin wadannan lokuttan bisa ga al’ada, samari kan yiwa ‘yanmata dinkuna da wasu hidindimu, amma mafi akasarin lokutta wadannan samarin, sukanje hutun naki, wanda sai bayan karshen wannan bukukuwan sai saurayi ya dawo, ko kuwa haka kawai sai saurayi ya kirkiri fada idan ana gabda wadannan lokuttana bukin sallah, da na maulidi. Wanda idan suka bata a wannan lokacin, to kaga babu maganar ya siya mata wadannan kayan. Amma bayan wadannan lokuttan shagulgulan sai a dai dai ta, duk wannan ba wani abu bane, illa hanyoyi ne da samarin kanyi amfani da ita wajen gujewa kashe kudi ga ‘yan matansu. Sukuwa wasu sunaganin wai wata hanyace ta gane koda yarinya tana sonka.