Masu iya magana kance, Hakuri gishirin zaman duniya, duk mai hakuri zai dafa dutse yasha romonshi. Abun fahimta annan shine, azumi wato wani ginshiki ne na tafiyar da rayuwar dan’adam, wanda said a hakuri ake cin ribar wannan rayuwar.
Kwamandar Hizzba ta mata, Malama Zara’u Umar, tayi karin haske dangane da muhimmancin yin hakuri musamman ma a wannan wata na azumi, wanda tace mafi akasarin mutane basu daukar koyarwar manzon rahama, da yake kira da mutane su maida hankali wajen kyautata ma iyalansu, dama sauran abokan mu’amala a kowane lokaci. Mafi akasarin mutane a cikin wannan watan sai ka gansu suna fada ko hayaniya, a cikin wannan watan fiyema da sauran watanni. Wannan kuwa ya sabama koyarwar wannan watan.
Don haka yakamata mutane su sani fa, shi azumi ba wai kawai kebewa daga cin abinci da mawasu abubuwa shine azumi ba, yakamata su san dacewar shi azumi ya hada da hakuri dama yadda mutane ke gudanar da mu’amalarsu da mutane, duk wadannan sune koyarwar azumi, da yakamata ace mutane sunci ribarshi. Kana kuma da kwadaitar da ma’abota bibiyar wasu addinai suyi sha’awar wannan addinin. Lallai yakamata mutane su surari malamai a wajen wa’azi da kuma kokarin aiki da wannan koyarwar ta manzon rahama.