Tashe Babbar Al'adace a Kasar Hausa

Tashe

Wata dadaddiyar al’ada a kasar Hausa a watan ramadana itace, ta yin “Tashe” wato shi dai tashe anayinshi ne domin nuna murnan kaiwa goma ga watan azumi. Matasa, yara, manya, mata da maza, na haduwa a lunguna da sako, na kowace anguwa ana kade-kade da wake-wake masu ban sha’awa, tare da bada abun masaruhi ga masu gudanar da wannan tashen.

A kan gudanar da wannan abubuwan nishadin ne a inda mutane suke, a basu dariya da duk wani abu da zai nishadantar. Kana kuma yananuni da irin al’adu dama nuni da jindadin wannan wata mai alfarma.

Amma a zamani irin na yanzu, ansamu akasi, tabakin wasu mutane, tashe nada, dana yanzu ya banbanta matuka, wanda shi tashe a da anayinshine cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma da mutunta juna, masuyin tashe sunayi ne don su sa mutane dariya kuma su sama abun kashewa a cikin watan azumi. Amma yanzu sai ka ga yara na kokarin tilastawa sai anbasu wani abu, to wannan ya sabawa ainihin al’adar mutan da.

A tabakin wani, tashen da akeyi yanzu bashi da suran armashi kamar na da, wanda da idan ana tashe yara idan sukazo inda ake sallah, to za’a tsaya har sai an wuce koma anyi salla, amma yanzu babu duk wadannan abubuwan. To gaskiya wannan yasabama ainihin al’adar da don haka kuma baza’asamu wani abun nishadi a cikin shiba.