'Yan Civil Defence Sun Masa Duka Har Ya Mutu A Sokoto

Jamilu Abdullahi, dauke da alamun dukar da 'yan Civil Defence suka yi masa a Ofishinsu na Sokoto South

'Yan hukumar tsaro da kare rayukan fararen hula ta Najeriya, wadda aka fi sani da sunan Civil Defence, sun lakkada ma wani bawan Allah mai suna Jamilu Abdullahi duka har sai da ya mutu a ofishinsu na Sokoto ta Kudu.

Wata mace mai suna Amina ce ta gayyato 'yan Civil Defence, watakila a saboda akwai wata alaka a tsakaninta da su, suka tafi da shi Jamilu ofishinsu, a bayan wata cacar bakin da ya shiga tsakaninta da shi. Bayan sun masa wannan duka ta cin zarafin ne suka kai shi asibiti, inda ya cika.

Jamilu ya rasu tun ranar 5 Yuni, amma har yanzu gawarsa tana asibitin koyarwa na jami'ar Usman dan Fodio a Sokoto, a saboda wai su na bincike.

A kasance da filin Ciki da Gaskiya domin jin cikakken bayani na irin wannan rashin imani na ma'aikatan da aka dora ma alhakin kare rayukan mutane da dukiyoyinsu.