Ai Demokaradiyya Idan ba Matasa Wasa ce

Matasa

Abubakar Muhammad, shugaban kungiyar kare hakin bil’adam ta CMDD, yayi korafi akan yadda gwamnatoci ke jinkirin nada matasa a mukamai da zasu bada tasu gudunwa, yace duk da sanin cewar wannan gwamnatin a wannan zamanin zasuyi da matasa, to amma abun na tafiya mahauniya. Sanin kowane cewar wannan siyasar yanzu, bakowane yayi wannan zaben na wadannan shuwagabannin ba, ilaa matasa don haka su yafi dacewa da abama kaso mafi yawa.

Dalili kuwa shine mai daki shiyasan inda ruwa ke masa zuba, ashe kenana su matasanan su sukasan mecece matsalarsu, dakuma wace hanya yakamata abi wajen magance ta, a kuma wane irin yanayi suke. To lallai ya kamata ace gwamnatoci a kowane mataki, su tashi tsaye wajen ganin sun bama matasa matukar kulawa, don a samu ayi dai daito a wajen kawo cigaban kasa da al’umah baki daya.

Abun kara jawo hankalin matasa a nan shine, yakamata su tashi tsaye wajen ganin sunyi amfani da duk wata dama da aka basu, wajen kawo cigaban kasa da ma ‘yan’uwansu matasa a kowane mataki, kada su dauki al’adar daga ni sai ‘yan’uwana, donmin wannan dabi’ar bazata haifarwa kasar d’a mai ido ba. Don haka yanzu dubara tarage a tsakanin matasa, su san yadda yadace su fito da wasu tsare tsare da zasu taimakama wajen ciyar da kasa gaba a duniya.