A kusan karon farko malamai a jamia’ar A&M Texas ta nan kasar Amrka, sunyi yunkurin kada dalibai a jarabawa baki daya, bisa ga dalilin da suka kira rashin da’ar dalibai ga malamai a yayin da ake gudanar da darasi a aji.
Amma hukumar makarantar tashiga wannan maganar da zummar dai-daita tsakanin malamai da dalibai, a tabakin daya daga cikin farfesoshin, ya bayyanar da cewar wadannan daliban basu datarbiyya ko kadan, basu yin aikin dai dai da yadda yakamata.
Sai ya kara da cewar, wadannan daliban, basa darajashi a matsayinsa na malami, don haka yana ganin bai kamata ace har sun iya kamala karatunsu na jami’a ba, dalili kuwa shine, idan akace dalibi ya kamala karatun jami’a yasamu aiki, sai aka sameshi da rashin da’a a ma’aikata, abu na farko da za’a fara tambaya shine, wai wace jami’a yaron ya gama ne?
Daga nan sai a ambato sunan makrantarsu. To kaga daga nan za’aga cewar malamansu basu koyar da su yadda ya kamata ba, a karshen laifi zai dawo kan malamai na cewar basu koyar da su yadda yadace ba.