Rashin aikinyi yazamo babban kalubale ga matasa a duniya, musamman ma a Najeriya, aikinyi wani babbana abune da yafi shafar matasa. Alkalumma sun nuna cewar kimanin kashi sittin na yawan al’umar Najeriya, matasa ne wadanda suke tsakanin shekaru gomasha takwas zuwa talatin 18-30, akasarin wadannan matasan da wadanda sukayi makaranta da ma wadanda basuyi ba suna fama da rashin aikinyi.
Wasu daga cikin irin abubuwanda kan kara yawan rashin aikinyi a kasar shine, yadda wasu kamfanoni kan salami ma’aikatansu a kowane irin yanayi, Bashir 'Yalleman, wani matashi ne wanda ya samu dammar kamala karatunshi na Difiloma, kuma yana aiki da Kamfanin Soject, wadanda suke kan aiki a wannan gadar da ta fado a unguwar Dorayyi, a kwanakin baya a jihar Kano. A wannan sanadiyar fadowar gadar da tayi sanadiyar mutuwan wasu mutane, yasa an dakatar da kamfanin.
Ya kara dacewar kimanin sama da mutane dari biyu da sittin 260, ne suka rasa aikin yi a wannan sanadin na dakatar da kamfanin, wanda wannan ba karamar illa bace ga karfin tattalin arzikin jihar. Kana wannan wani babban kalubale ne ga wadanda suka rasa wanna aikin, domin kuwa wasu basu da halin da zasu iya ciyar da iyalansu, to a zahirin gaskiya wannan kan iya sa wasu matasa su fada cikin wani hali da bashi da amfani. Don haka muna kara kira ga hukumomi da masu hannu da shuni dasu taimaka su sama ma matasa aikin yi don gujema wasu abubuwan da matasa kan sa kansu a ciki.