Watan Azumi Watan Karin Lafiya da Shan Abubuwan Gina Jiki

Kayan marmari

Mafi akasarin mutane sukan manta da mahimancin watan ramadana, musamman ma ‘yan kasuwa, domin a watan ramadana ne mafi akasarin mutane sukan siya kayan gwari, wato don su samu abubuwa masu gina jiki, amma a kuma wannan watan akan samu banbancin farashi da kan kai kimanin kaso da dama. A yayin da wasu kamfanoni da wasu masu hannu da shuni ke kokarin rangwanta kayyayakinsu su kuma wasu suna kokarin tsauwalawa.

Malama Mustapha, wani mai sana’ar saida su lemu, ayaba, abarba, kankana, da dai sauransu na fuskantar chanji na farashi da yakai kimanin kashi dari, banbanci da yadda suke sayo da siyar da kaya a wannan watan, wannan nasa mutane cikin matsuwa kwarai da gaske, don kuwa wasu basa iyasamun dammar siyan wadannan abubuwan yadda yakamata, a sanadiyar tsadar wadannan kayan.

Masu sana’ar gwarin dai sun koka kwarai da gaske, don suna ganin yakamata ace wannan watan ne yadace kowane irin kaya su sauka, don masu karamin karfi su samu dammar da zasu iya siya, amma sai ga akasin hakan. Don haka suna kara kira ga masu sana’ar motoci dasu taimaka su rage kudin dakon kaya daga wani yanki zuwa wani yanki, wanda tahakan zai sa kayan su rage matuka. Kuma suna ganin akwai bukatar gwamnatoci su sa hannu wajen ganin a daidaita farashin kaya a kowane mataki, wanda tahaka za’a iyasamun tattalin arzikin kasa mai yalwa.