Na fahimta matuka da mahimmancin gabatar da kai cikin amintaka. Wani dalibi mai karatun digirin digirgir a jami’ar Kimiyya ta Massachuset, ke bayyanar da haka.
Mr. Jake Livingood, ya gabatar da wata kasida, inda yake bayyanar da cewar, lallai yana da matukar mahimanci idan malamai a matakin firamari da sakandire, zasu fito da tsarin bama dalibansu damar su dinga gabatar da wasu bincike nasu, kuma su bayyanar da sakamakon bincikensu a gaban aji, ko kuwa su dinga magana a gaban dalibai yan’uwansu a kowane lokaci. Wannan wata damace da zata taimaka ma dalibai su zamo masu basira, kwarjini, iya magana, rashin tsoro wajen bayyanar da gaskia da dai makamantan hakan.
A nashi iya binciken, ya gano cewar lallai idan akasa wannan tsarin cikin manhajar karatu a matakin firamari da sakandire, ba shakka zai tallafawa yara tun suna kanana wajen samun kwarjini da iya zaman takewar yau da kullun kamin su girma. Yana da yakinin cewar, idan dalibi daya yasamu kwarin gwiwar yin hakan to saura ma na iya bin sahunshi, ta haka sai a samu al’umah mai nagarta.