Anawata ga wata, ina samari matasa daga shekaru gomasha bakwai zuwa ashirin da biyar? Kuzo ga wata garabasa. Wata kyya-kyawar buturwa ‘yar shekaru ashirin da biyu 22 na neman miji, Taibat Hafsat Abdulmumin, ida dai tace ba tana tallar kanta bane, illa dai saboda wani tsohon saurayinta daya yaudare ta abaya ne shiyasa take neman miji wanda yake da mutunci da kamala ta aura don ta huce takaicin wancan saurayin nata. Wanda tace duk namujin da yasamu nasarar zama mijinta, zata bashi kyautar mota kirar Honda da tankacecen gida a matsayin tukicin aurenta.
A rahoton da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, ta hada muna inda wannan baiwar Allah take bayyanar da irin mijin tda take so, tana son namiji wanda yasan mutuncin mace da kuma sanin yakamata kamin ta aureshi.
Daruruwan matasa sun kure adakarsu, sun kumayi turururwa zuwa gidan radiyon da ya bayyana wannan labarin tun da misalin karfe bakwai na safe don neman lambar wannan yarinyar da zummar su gwada sa’ar su. A tabakin wasu da ta zanta da su, daya daga ciki nanuni da cewar shi gaskiya yanason yayi aure tun kamar shekaru da dama, kuma yana da sanar shi amma bashi da kudin da zaiyi aure, shiyasa bai damu kanshi ba., amma wannan wata damace idan yasamu zai yi amfani da ita don yayi auren shi.
Shi ma wani da ya bayyana nashi ra’ayin, cewa yayi shi gaskiya baya bukatar motar ta da gidanta, shidai kawai yana son tada aure ne, wanda idan yasamu wannan dammar zai so ya aureta. Cin cirindon mutane nata kaikawo wanda wasu ma har sun bada hotunansu don a ba wannan yarinyar dagani idan sunyi mata.