Tsaftar Muhalli Tsaftar Aljihu ga Matasa

Umar Idris Mai Bola

Tsafttace muhalli wani abu ne da ke da matukar mahimmanci ga rayuwa al’umah. Hakkin jama’a ne su tabbatar da sun tsafttace cikin gidajensu da kewaye, wannan wata hanyace da za’a iya samama matasa sana’ar yi tun suna ‘yan kananan, su saba da nema don zama wani abu a rayuwa.

A irin kwazo na Umar Musa Idris, wanda yake yaro ne mai shekaru goma sha shida 12, kuma yana makarantar firamari ne a yanzu haka, ya sama wa kanshi sana’a wadda zai dingayin lalurorinshi batare da ya tambayi mahaifansa ba, yana ganin cewar tunda har sun sashi a makaranta to yakamata ace yana nashi kokarin wajen taimaka musu, da ma kanshi wajen siyan wasu abubuwa.

Ya kirkiri wata dabi’a ta bi gida-gida yana tambayar idan mutane na da bukatar a kwashe musu bola don kaiwa jeji a zubar, wanda ana bashi kudi kuma yakanyi amfani da kura wajen kwasar bola mai yawa a lokaci daya. A wannan sana’ar Umar dai yakan samu kudi kimanin naira dari biyu har zuwa dari hudu a rana, yakan tara wadannan kudin nashi a bankin asusu ne, wanda a duk lokacin da ya bukaci yayi wata lalura ko ya taimaka ma iyayenshi, sai a bude wannan bankin don diban kudin.

Wato babban abun sha’awa da Umar shine yaro ne da ya’iya gane cewar tunda iyayenshi sunyi mishi duk abun da yakamata na sa shi a makaranta, to lallai yakamata shima ya samar da wata hanya da zai iya tallafama kanshi da su don rage musu wasu nauyin. Don haka iyaye su tashi tsaye wajen koyama ‘yayansu sana’a tun da kuruciyar su kamin su san zama manyan mutane.