Tsarin Tallafin Ilimi Kyauta Bai Kaiwa ga Kowa

Kwalejin kimiyya da fasaha

A irin cigaba da kasashen duniya sukayi, tsarin ilimi kyauta na daga cikin abubuwan da sukasa wadannan kasashe suka samu daukaka a duniya. Abu da yakamata ace yanzu a kasa irin ta Najeriya, yakamata ace an wuce matakin bada ilimin firamari, sakandire, kyauta yanzu kamata yayi kowace jiha tana iya bama dalibanta ilimi kyauta a kowane mataki, wanda ta haka ne kawai za’a iya samun cigaban kasa.

Ana cikin haka sai ga wasu matasa na koken cewar basu cikin tsarin bada ilimi kyauta, na jerin tsarin bada ilimi kyauta na asalin ‘yan jihar Kano, wadannan matasan na kokawa da babbar murya da gwamnatin jihar, ta duba wannan tsarin da kyau don ta taimaka musu, su samu su kamala karatunsu cikin sauki.

Su dai wadannan matasan suna karatune a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano, sun bayyanar da cewar su basa samun kowace irin tallafi da ga gwamnatin jihar, amma suna da masaniyar cewar gwamnati tafito da wani tsari na bama kowane dan asalin jihar ilimi kyauta, amma suba suga wannan tsarin ba, don haka suna kira ga shuwagabannin da su duba wannan al’amarin don suma a basu damar moriyar arzikin jiharsu.