Hanyar Samar da Ingantacciyar Lafiya Dayace

Muhallai masu tsafta

Tsafta wata abace mai matukar mahimanci ga rayuwar dan’adam, sanin kowane cewar duk inda bai da tsafta to yana da matukar damuwa ga lafiyar dan’adam harma da na dabobi.

Alal hakika, bincike da masana suka gudanar na nuni da cewar babban umul haba’isin kowace cuta na da alaka da rashin tsafta, ta haka ne cuta kansamu wajen zama a cikin al’uma.

Musamman ma cutar kwalara, zazzabin cizon sauro, da dai ire-irensu, don haka yana da matukar mahimanci mutane su sani cewar, ya kamata su maida hankali wajen tsaftace muhallan su don samun ingantacciyar lafia ga iyalan su.

A tabakin Malam Umar Sale Anka, mataimakin shugaban masu kula da muhalli ta kasa, reshen jihar Kano, wanda ya ke bayyanar da bukatar a samar da hukuma da zata tabbatar da an tilastama jama tsaftace muhallansu. Don ba hakin gwamnatoci bane kawai su dinga samar da tsaftataciyar muhalli ga kowaba, suma al'uma nada nasu rawar ganin wajen tabbatar da lafiya da tsaftar muhallansu a kowane yanayi, a lokutta da dama gwamnatoci na kokari, amma saboda rashin kulawa irin ta mutane sai a cigaba da samun yanayi mara magarta.

Don haka yakamata mutane su maida hankali wajen tsaftace cikin gidajensu dama anguwanni kada a jira sai gwamnatoci sun zo kamin a tsaftace wurare, don wannan ma kamata yayi a rataya wannan hakin ga mutane anguwa, su kuma gwamnatoci su taimaka wajen cigaba da samar da nagartattun wajajen zubarda shara da kayan aiki ga jama, wanda ta haka ma gwamnati na iya samar da aikinyi ga masa.