Ashe Kuwa Zaiga Balbalin Bala'i

Daurin Aure a

Anya kuwa wai tsakanin maza da mata wai wa yafi kishi ne? Wasu matasa da suka bayyana ra’ayin su a kan wanda yafi kishi, wata da ta bayyana nata ra’ayin cewar lallai idan har ta kasance tana kyautata ma wannan mijin nata, kuma ya kasance babu wani abu da takeyi masa da zai sa ya kara aure, to lallai daga ranar da yayi maganar kara aure, zai ga balbalin bala’I kuwa, don bazata taba barinshi zaman lafiya ba.

Don a gaskia tana ganin yaza’ayi ace tanaraba mijinta da wata. Ai idan har yanason ta, to ba zaiyi tunanin ma auren wata ba gaskia. A bangaren maza kuma suna ganin, ai ba wai sai bakason matarka ne kawai zaka kara aure ba, tunda dai wannan bai sabama addini ba to kawai yakamata ace su mata su dinga fahimta, shigowar wata bai sa ace baya sonta kokuma ya muzguna mata, abun da yakamata ace mata sun dinga yi shine daga ranar da akace wata zata shigo, to kamata yayi su dinga kokarin kyautata masa don shima yayi kokarin sonsu yadda yakamata.

Amma a wasu lokutta sai kaga wannan lokacin ne suke maida wa lokacin tada hankalin mai gidan harma ya kaiga rasa tunaninsa a sanadiyar wannan hali nasu matan. Babban abu a nan shine yakamata mata su maida hankali wajen kyautata ma mazajen su da kuma abokan zamansu "Kishiya" haka suma maza suyi kokarin yin adalci a tsakanin matansu don neman gamawa da duniya lafiaya baki daya.