Wannan wani zamani da al’uma ke ciki, wani zamani ne da yake da ban’al ajabi, idan akayi la’akari da wasu shekaru goma shabiyar da suka wuce a baya dai mutane basu zama sun saba da hurda da abubuwan zamani ba, amma a wannan zamani da muke ciki, mutane sun zama basu iya gudanar da rayuwarsu ba tare da wadannan abubuwan zamanin ba.
A wani bincike da wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir, ta gudanar a tsakanin matasa, wadannda sukayi karin bayani kancewar basu iya gudanar da rayuwar su batare da suna rike da wayar su ta hannu ba, to abun tambaya a nan shine, wai kuwa matasannan na amfani da wannan wayoyin na zamani ta hanyar da suka dace kuwa? A tabakin Usman Audu, wani mai yima kasa hidima wanda yake gani lallai bazai iya rayuwa batare da wannan wayar tashi ba, don da ita yake sada zumunta da iyayenshi da abokan arzikin a garinsu, don ya kasance yana wata jihane inda yake gudanar da aikin bauta ma kasar. Sai itama Aisha Muhammad, wadda take ganin ai idan bata da waya to bata da rabin jikin ta don ta wayar ta take samu labaran abubuwan da ke farukwa a duniya, musamman ma ta yanar gizo, a shafinta na facebook, twita da dai makamantansu.
Babban abun jan hankali a nan shine, matasa suyi kokarin yin amfani da wannan damar tasu wajen yada manufofi masu alfanu ga cigaban matasa da cigaban kasa baki daya, wanda ta hakane kawai za’a iya samun dauwamamar kasa baki daya.