Cin Hanci a Matakai Daban-Daban

EFCC

Rashin aikinyi wani babban al’amari ne a daukacin Najeriya, baki daya. Sanin kowane cewar akowane lokaci ‘yan siyasa na alkawalin samama matasa aikin yi idan aka zabe su. Sai gashi a jihar Kano, wata sabuwa ta billo, inda ake tatsan matasa marasa aikinyi kamin a basu aiki. Wasu matasa a jihar na bayyana yadda aka bukace su da ko su chanza sunansu kana kuma su bada abun goro kamin a basu aiki.

To babban abun damu a nan shine yadda ake nuna banbancin kabilanci ko addinanci a wajen neman aiki ko bada aiki, wannan babban kalubale ne ga cigaban kasar, musamman ma ta yadda wannan zai yi alfanu a wajen rabakan ‘yan kasa.

Ya kamata ace gwamnatoci a kowane mataki su mai da hankali a yadda kamfanoni masu zamankansu suke gudanar da harkokin daukan ma’aikatan su da kuma hakokin ma’ikata ba lallai na gwamnatiba. Kuma gwamnatoci su sani da cewar akwai masu karbar na goro da yawun gwamnati kamin a bama mutun aiki, don haka yazama wajibi, sukan su matasa su nemo hanyar dogaro da kai ba kawai su dinga dogaro da gwamnati ba, domin kuwa gwamnati bata isan al’uma baki daya batare da taimakon matasa ba.