Yau 8 Ga WataTake Ranar Tekuna

'Yan gudun hijira a Yemen suke shiga wani jirgin dakon mai.

Wannan rana dai 8 ga watan Yuni rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin kara maida hankali kan tabbatar laifyar tekuna.

Taken bikin na bana shine "Idan Tekuna suna da koshin lafiya, Duniya ma zata sami lafiya".

Wannan rana ce da kungiyoyi da 'yan gwagwarmaya suke bukukuwa da zummar kara jawo hankali kan bukatar daukan matakai da zasu inganta lafiyar tekuna.

Ibrahim Ka'almaseeh Garba ya tattauna da wani dan gwagwarmayar rajin kare tafkin Cadi, Ishaya Buba, wanda yayi magana kan fa'idar kare tekuna.

Daya daga cikin zummar bukukuwa na bana shine hana cushe tekuna ko koguna da ledoji.

A nasa bangaren, Mallam Ishaya yace, wannan rana ce suke kara kulawa da matsalolin gurbacewar tekuna, da kuma yadda al'uma suke amfani da shi. Shin ana kulawa da ruwayen a matsayin abunda zai dore, kodai ana yi ne kamar babu gobe.

Haka nan ana amfani da wannan rana wajen tattaunawa kan batutuwan tsaro cikin ruwa, ganin ana samun mafasa wadanda suke kassara ayyukan sifiri dana kasuwanci.

Da ya juya kan tafkin Cadi, Mallam Ishaya yace tafkin ya fuskanci mummunar barzana na karewar ruwa, alamarin da yasa kasashe dake amfana da tafkin, daga Najeriya, da Nijar, da Cadi, da Kamaru d a sauransu suka hada karfi wajen ganin an samu wata hanya ta shayar da tafkin, sanin mashayunta sun fuskanci damuwa saboda sauyawar yanayi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar tekuna