A wasu bincike da aka gudanar dake nuni da cewar shan taba sigari na da matukar illa ga rayuwar mashayanta, kai harma da masu kusantar mashayan. Cutar da taba sigari kan haifar na da nau’I daban daban. Dr. Ashiru Adamu, wani masanin kiwon lafiya, yayi muna karin haske a kan illolin shan taba.
Wanda yake cewar ita taba ba wai kawai tana lalata huhun dan’adam ne kawai ba, tana sama mutun wasu cututuka da mutun kan iya manta abubuwa a sanadiyar, wannan tunanin na cewar idan mutun ba shaba zai ji cewar kamar jikinshi bai cikaba. A irin wannan halin sai ka ga mutun ya samu kanshi a wani irin hali, kuma babban abun damuwa a nan shine, duk wanda ya zamana yana shan taba wanda har idan kimanin yawan tabar tayi mishi yawa a jiki, to zai iya gurbata wasu sinadarai a cikin jikin dan’adam.
Don haka yana kira ga al’uma musamman matasa da su guji sha’awar shan taba, don wannan hali ba zai haifar musu da wani abu ba illa cutar da jikinsu, wanda daga bisani ko a gaba zasu ga rashin alfanun, haka don za suga masu irin shekaru nasu basu samu matsaloli a rayuwa ba musamman a shekarun tsufa.