Amurka Da Wasu Kasashen Yammacin Duniya Suna Shirin Horasda Dakarun Najeriya.

Shugaba Buhari da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.

Hakan ba zai rasa nasaba da kafa sabuwar gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Wani tsohon jakadan Najeriya a kasar Spain da fadar Vatican, Ambasada Yusuf Mamman, ya bayyana godiya ga irin alkawuran da Amurka da tarayyar turai suka yi na taimakwa Najerya musamman ta fuskar tsaro.

Ambasada Mamman ya bayyana fatar wannan dangantaka zata dore, wajen ganin Najeriya ta ceto 'yan matan Chibok wadanda 'yan kungiyar Boko Haram suka sace suke garkuwa da su yanzu fiyeda shekara daya.

Dangantaka tayi kamari tsakanin Amurka da Najeriya, a yaki da Najeriya take yi da 'yan tada kayar baya a arewa maso gabashin kasar. Amurka tana zargin dakarun Najeriya da keta 'yancin Bil'Adama a fafatawar da suke yi da 'yan binidgar. Wasu suna ganin wannan zargi yana daga cikin dalilanda suka sa Amurka taki sayarwa Najeriya makamai.

Shima jakadan canada a Najeriya John Calderwood, ya bayyana anniyar gwamnatinsa wajen aiki tareda sabuwar gwmnatin kasar a fannoni daban daban kama daga tsaro, da zummar zurfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Ga rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Difilomasiyya karkashin Buhari