A dai dai lokacinda tsohon shugaban mulkin soja, kuma zababben shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya fara bayyana irin mutane da ya zaba suyi aiki tare, ana jin shugaba Buhari, zai fi maida hankali kan tsaro, da farfado da karancin wutan lantarki, da samar ayyukan yi ga dubban matasa.
A kokarin warware karancin wutan lantarki, tsohuwar gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta sayarwa 'yan kasuwa tashoshin samarda wutan lantarki. Amma wasu suna ganin hakan bai warware wannan matsala ba, saboda haka suke son ganin gwamnati ta karbe wadannan tashoshin.
Amma daya daga cikin masu kamfanonin da aka sayarwa tashoshin Ka'yinji da Jebba, kanal Sani Bello mai ritaya, yace matsalar ba daga kamfanonin suke ba. Yace wutan lantarki da suka samar ba'a bari su tura hasken, domin gudun karfin wutan lantarki zai karya hanyoyin, don sun tsufa.
A yanzu haka suna bin gwamnati Naira Bilyan 7, na wutan lantarki da suka samar.
Ahalinda ake ciki kuma, Bankin duniya ya samarda dala milyan $300 domin samar da ayyuakn yi ga matasa.
Shugaban shirin na jihar Niger Akilu Musa Kuta, yace shirin ya zama wajibi saboda samarwa matasa aikin zai kawo zaman lafiya.
A nasa ran matasa dubu 91,000 ne zasu amfana karkashin shirin.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5