A yayinda ake cigabada gunarar da bukukuwan rantsar da sababbin gwamnatoci a jihohin Najeriya, an dai samu nasarar kamala wadannan bukuku a wasu jihohi, wanda a wasu kuwa abun basuyi dadiba.
Rahotannin daga jihar Naija, babban birnin Minna, inda aka gudanar da rantsar da zababben gwamna Alh. Abubakar Sadik Sani Bello, wanda tsohon gwamna mai barin gado Dr. Babangida Aliyu, yasha ruwan duwatsu, wanda daker aka fita dashi daga filin rantsarwar.
A tabakin wasu, suna ganin wannan yasamo nasaba da yadda tsohon gwamna ya gudanar da mulkinshi a jihar, wanda ke nuni dacewar bai kyautatama mutane jihar tashi ba. Kuma wasu na ganin zai bar gwamnatin da dunbin bashi da zai barma sabon gwamnan.
A tabakin tsahon kwaminshinan labarai na tsohuwar gwamnatin Malam Dalladi Inda Yaba, ya musanta wannan zargi da akeyi na cewar sunbar basusukan makudan kudi. Shima tsohon gwamnan jihar Kano, a mulkin soji Kanal Aminu Isah Kwantagora, yayi tsokaci da cewar lallai wannan gwamnatin mai shudewa batayi abun da ya dace da itaba shiyasa tasamu irin wannan sakamakon daga al’umar ta, sai dai yana kira ga shuwagabannin da suyi la’akari da irin wannan don yazamo musu darasi a gaba.