Hukumomi a kasar Switzerland da nan Amurka sun damke mutane 14 dangane da zargin cin hanci da rashawa mai alaka da zabenh kasashe 3 da zasu dauka ko suka dauki bakuncin gasar cin kofin kwallon kafar duniya da kuma wasu wasannin kwallon kafa a wasu kasashen nahiyar Arewaci da ta tsakiyar Amurka. Wakilin Muryar Amurka yace an kama jami’an hukumar FIFA su 7 tare da shugabannin wasu kamfanoni 5.
Yau laraba da asubahi ‘yan sandan Switzerland suka kai sumame kan wani hotel a birnin Zurich, inda jami’an FIFA suka taru domin taron shekara na hukumar.
Jami’an da aka kama sun fito ne daga hukumomin kwallon kafa na kasashen nahiyoyin Amurka ta Arewa da ta Tsakiya da kuma yankin tekun Carribean, wanda Amurka take tuhuma da laifin karbar cin hancin miliyoyin daloli dangane da bayarda lasisin watsa wasanni na yanki mai room sosai, da kuma batun zaben kasar Afirka ta Kudu a zaman wadda ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekarar 2010.
Su kuma masu gabatar da kararraki na Switzerland sun kara da nasu tuhume-0tuhumen dangane da yadda aka zabi Rasha ta dauki bakuncin gasar cin kwallon kafar duniya a 2018 da kuma Daular Qatar a zaman wadda zata karbi bakuncin gasar a 2022.
Anyi zargin cewa an shafe shekaru 24 ana tafiyar da wannan aiki na karbar cin hanci da rashawa.
Wadanda ake tuhumar dai ‘ya’yan wasu kasashe 10 ne na Latin Amurka da Carribean da nan Amurka da kuma Britaniya.
Amma kuma wadannan tuhume-tuhume bas u shafi shugaban hukumar kwallon kafar duniya, Sepp Blatter, wanda ya shafe shekaru 17 yana jagorancin FIFA ba, wanda kuma a jibi jumma’a yake fuskantar zaben sake ci gaba da rike wannan kujera.
Kakakinsa, Walter De Gregorio, yace wannan tuhumar ba wai ma hukumar FIFA ake yi ba, ana yinta ne a kan mutanen dake jagorancin hukumomin kwallon kafa na wasu yankuna, wadanda kuma suna cikin majalisar gudanarwar FIFA. Yace wannan laifin an aikata shi ne a kan FIFA, kuma kama mutanen zai taimakawa hukumar wajen yakar zarmiya da cin hanci.
Abinda ya faru mai kyau ne. Hakan ya tabbatar da cewa muna kan hanya. Abin bakin ciki ne, ba abu ne mai sauki ba. Amma yadda ya kamata ke nan ayi.
Kakakin ya kuma yi watsi da kiran da wasu keyi cewa Blatter yayi murabus. Abokin adawarsa a zaben na jibi jumma’a, Yarima Ali bin Hussein na kasar Jordan, ya bayar da wata gajeruwar sanarwa a rubuce yana fadin cewa wannan ranar bakin ciki ne ga duk mai sha’awar kwallon kafa. A can baya, Yarima Ali ya sha nanata abinda zai bada hankali kai idan an zabe shi…
An sha yin amfani da Kalmar nuna gaskiya a bayyane. Yanzu tilas a aiwatar da hakan. Kuma in a bayarda tabbacin cewa za a yi hakan.”
Wani jami’in ma’aikatar shari’a ta Amurka dake kula da wannan bincikjen, yace kama wadannanmutanen bas hi ne karshen batun ba.