Wani abu da yakamata ace matasa musamman mazauna kasar Najeriya su sani, shine cewar babu wata kasa da takaimu su kasarsu. Duk wani abun kyale-kyale da sukan gani a wasu kasashen duniya kada ya rudesu, ko kuma ya basu sha’awa. Wani muhimin abu da yakamata su maida hankali a kai shine taya zasu zamar da tasu kasar wata abun tunkaho a duniya, ba kawai ace su tunaninsu na barin kasar ne kawai.
A wasu lokutta matasa maza ko mata kan bar kasashen su da zummar zuwa wasu kasashe don neman abun duniya, wannda daga bisani sukanshiga wasu munanan halaye, to babban abun da yakamata matasa su sani shine, suma kasashen da suka cigaba sai da suka bi wadannan hanyoyin kamin su zama abun da suke yanzu, don haka yakamata ace matasa suyi zummar ganin sun taimakama kasar su ba barin taba.
A tabakin shugaban yanki na hukumar yaki da fataucin bil’adam na jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, Malam Hassan Hamisu Tahir, yace hukumar su tana aiki tukuru wajen ganin sun dakile wadannan dabi’u da wasu miyagun ‘yan kasar keyi, wajen safarar mata da yara don zuwa wasu kasashe don bauta da fasikanci. Yanzu haka hukumar su ta tanadar da hukunci mai tsanani ga duk wanda akasamu da wannan sana’ar ta fitar da mutane, batare da wasu manufofi masu ma’ana ba. An tana dar da hukuncin sama da shekaru goma a gidan kasu ga duk wanda akasamu da wannan.