Koyon Yadda Ake Hada Fina-Finai Zai Tai makama Matasa

Sana'ar editin

Mansur Musa Alhasan, wani matashi ne wanda ya dauki sana’ar editin na bidiyo, a matsayin wata abu da yakamata ace matasa sun maida hankali wajen bunkasa harka.

Ya kasance yanayin wannan sana’ar kuma yana karatun a jami’a, kana kuma wannan aikin nashi bai hanashi ci gaba da karatunshi ba da wasu harkokin yau da kullun. Hasalima yana ganin cewar wannan wasu kalubale ne na rayuwa da yakamata ace kowane matashi ya fuskanta wanda ta haka ne kawai zai iya, sani wai menene rayuwa.

Ya kara da cewar, ita dai sana’ar editin mafi akasani matasa basu wannan sana’ar kuma wata sana’ace da zata iya taimaka ma mutun ya fahimci rayuwar yau da kullun, mussamman ma saboda yadda ake gudanar da ita dai dai da zamani, kuma ta wannan sana’ar mutun zai kara samun ilimin na’urar zamani.

Don haka yana kara kira ga matasa ‘yan uwanshi da su duba wannan sana’ar don koyi da fahimtar alfanun da ke cikinta, kana da kuma neman hanyar da zasu bi don su taimakama kansu.