An zub da maza da dama jiya lahadi a wasannin lig-lig na Farfeshinal a Najeriya, inda daya daga cikin manyan kungiyoyin Najeriya, Enugu Rangers, ta sha kashi a gida a hannun kungiyar kwallon kafa ta Giwa FC ta Jos.
A wannan wasa da aka gwabza a filin wasa na Nnamdi Azikiwe dake Enugu, kungiyar Giwa FC ta bar ‘yan kallo baki bude a bayan da ta jefa kwallo guda mai ban haushi a minti na 50, lokacin da Shu’aibu Ibrahim ya jefa daga wani bugun kusa da gida. A yanzu kungiyar Giwa FC ta Jos ta shiga cikin kungiyoyi 5 dake saman wannan teburin lig na Farfeshinal a Najeriya.
Ita ma Wikki Tourists ta je har gida ta zubar da Abia Warriors da ci 2-1 a filin wasa na Umuahia. Yanzu Wikki Tourists sune na biyu a saman teburin lig suna da maki 7.
Kano Pillars ta doke Enyimba da ci daya mai ban haushi ita ma ta kafar dan wasanta mai suna Ubong Ekpai ana dab da tafiya hutun rabin lokaci. Yanzu Pillars ta ciro sama zuwa matsayi na 6 a teburin lig din.
Kungiyar Heartland it ace take saman teburin lig din a Najeriya inda a jiya ta je har gidan ‘yan Kwara United ta doke su da ci 3-1. Ahmed Jimoh na Kwara ya fara jefa kwallo, amma kuma Mohammed Mohammed da Jimoh Oni da kuma Bright Ejike na Heartland sun tsamo kitse a wuta, har ma da tsoka ma kungiyar tasu.