Za Ayi Ta Tsakanin Chelsea Da Manchester United

Duk da kyakkyawar abotar dake tsakaninsu, watakila gobe asabar za a yi dauki ba dadi idan kungiyar Chelsea dake karkashin Jose Mourinho ta kara da Manchester United dake karkashin tsohon maigidansa, kuma abokinsa Louis van Gaal, yayin da Chelsea ke ci gaba da kokarin daukar kofin wasannin lig na Firimiya na Ingila.

Van Gaal da ‘yan wasansa na Manchester United, zasu yi tattaki a goben zuwa Stamford Bridge, inda wasanni 7 ke nan bas u samu nasara a kan Chelsea ba.

Manajan Chelsea, Mourinho, yayi aiki karkashin Van Gaal a kungiyar FC Barcelona, kuma mutanen biyu sun ci gaba da kasancewa abokan juna, kamar yadda aka ga sun rungumi juna bayan kunnen dokin da suka yi a Old Trafford a watan Oktoba.

Idan Chelsea ta samu nasara, zata zarce kowace kungiya a saman teburin lig na firimiya da Maki 10, yayin da ya rage sauran wasanni 6 a kawo karshen kakar kwallo ta bana.

Ita ma Manchester United zata shiga wasan na gobe da karfin jiki, a bayan da ta doke QPR a ran lahadin da ta shige, kuma tana shirin komawa ga wasannin kofin zakarun kulob kulob na Turai a shekara mai zuwa bayan da ta doke abokiyar tsamarta Manchester City da ci 4-2, ta shige gaban City da maki 4 a teburin Firimiya Lig.