Ana Ci Gaba da Gwabza Gasar UEFA...Juergen Klopp Zai Yi Murabus

Kwach na kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund, Juergen Klopp.

Yau laraba za a ci gaba da yin karon batta a wasannin kwata fainal na lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai, inda Bayern Munich zata gwabza da Porto, yayin da PSG zata karbi bakunci FC Barcelona a birnin Paris.

Kungiyar Bayern Munich tana fama da matsalar rashin wasu ‘yan wasanta da suka j rauni, kamar David Alaba, Medhi Benatia, Arjen Robben, Frank Ribery, amma kuma ana tsammanin watakila zata iya kai labara idan ta ziyarci ‘yan Porto.

A wasannin farko guda biyu na kwata fainal da aka buga jiya talata na lashe kofin zakarun kulob kulob din na Turai, Atletico Madrid da Real Madrid sun yi kunnen doki a gidan ‘yan Atletico. Juventus, wadda take gida, ta doke AS Monaco da ci 1 mai ban haushi.

A mako mai zuwa, kungiyoyin takwas zasu sake karawa da juna a zagaye na biyu, kuma duk wadda adadin kwallayenta suka fi yawa zata haye zuwa ga wasan kusa da karshe.

A halin da ake ciki, yau laraba ne Juergen Klopp ya bayyana cewa zai yi murabus daga matsayinsa na manajan kungiyar Borussia Dortmund a karshen wannan kakar kwallon da ba ta yi dadi ma kulob din ba. Shekarunsa 7 yana jagorancin wannan kulob.

Dortmund ta yarda zata katse kwantarakinsa a ranar 30 ga watan Yuni, duk da cewa ya sanya hannu kan kwantarakin har zuwa shekarar 2018, watau akwai sauran shekaru 3 a wannan kwantaraki nasa.

Babu wani bayani da aka ji na wanda zai gaji wannan kujera.