WASHINGTON, DC —
Hukumar zabe ta Najeriya, INEC, tana dab da ayyana Barrister M.A. Abubakar na jam'iyyar APC a zaman wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Bauchi, a bayan da dukkan alkaluma suka nuna cewa ya doke Awwal Jatau na jam'iyyar PDP.
Sakamakon da hukumar ta bayar daga dukkan kananan hukumomin jihar ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar PDP ya lashe karamar hukumar kwaya daya tak ce, watau ta Bogoro, yayin da dan takarar jam'iyyar APC ya lashe duk sauran kananan hukumomi 19 na jihar.