An Kashe Mutum Guda, An Yi Harbe-Harbe A Kananan Hukumomin Jihar Rivers

'Yan Sanda a Jihar Rivers, Maris 30, 2015.

An samu harbe-harbe a yankunan kananan hukumomi da dama yayin da aka tabbatar da mutuwar mutum guda a tarzomar zabe a Jihar Rivers dake yankin Niger Delta a kudancin najeriya.

Rahotanni daga Fatakwal na fadin cewa an ga wasu 'yan daba a rumfunan zabe a wani matakin neman kuntatawa masu jefa kuri'a a kan su zabi wani dan takara dabam ko kada su zabi wani.

A cikin daren jiya kuma an bayar da rahoton canja mataimakin sufeto janar na 'yan sanda mai kula da wannan yanki bisa dalilan yin shisshigi cikin harkokin siyasa.

A kasance da www.dandalinvoa.com domin jin cikakken bayani kaitsaye daga Fatakwal tun daga karfe 3:15 na la'asar din yau asabar.