Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya nuna takaicinsa domin rashin cimma daidaituwa tsakanin shugabankasar Sudan Ta Kudu da madugun 'yan tawaye
WASHINGTON, DC —
Kwamitin Sulhu na MDD ya nuna rashin jin dadi da gazawar shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun ‘yan tawaye Riek Machar cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
A wata sanarwa da Kwamitin ya fitar jiya Talata yayi barazanar kakabawa wasu manyan jami’ai takunkumi,wanda ake kyutata zaton su ne suke hana ruwa gudu.
Wadannan manyan jami’an su ne suke kawo wasu manufofin dake kawo rashin jituwa a kasar Sudan Ta Kudu.
Yakin da yaki ci yaki cinyewa a wananan kasa mai albarkatun man fetur ya kashe dubban mutanen kasar ya kuma raba wasu fiye da miliyan biyu da muhallansu.