Matan Da Suka Kubuta Daga Hannun Boko Haram Sun Yi Bayani

Dubban mata da yara sun gudu zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira kamar wannan dake Bole, kusa da babban birnin jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin dake karkashin dokar-ta-baci. (VOA/Ibrahim Ahmed)

Yunkurin dakarun hadin gwiwa da suka kunshi dakarun Najeriya, da Nijar, da Kamaru da kuma Chadi dake yunkurin kakkabe 'yan kungiyar Boko Haram daga Gwoza ya fara cimma nasara.

Rahotanni na nuni da cewa, yunkurin dakarun hadin gwiwa da suka kunshi dakarun Najeriya, da Nijar, da Kamaru da kuma Chadi dake yunkurin kakkabe 'yan kungiyar Boko Haram daga Gwoza ya fara cimma nasara.

BInciken da wakilin Sashen Hausa Sanusi Adamu ya gudanar na nuni da cewa, mayakan kungiyar Boko Haram sun fara gujewa garin na Gwoza zuwa dajin Sambisa tare da sako mata da 'yammata da suke garkuwa da su.

Daya daga cikin matan da suka tsallake rijiya da baya, bayan sun shafe watanni biyu a hannun 'yan kungiyar Boko Haram, ta shaidawa wakilin Sashen Hausa, Sanusi Adamu cewa, ita da 'ya'yanta mata biyu na daga cikin matan da kungiyar ta tasa keyarsu da nufin aurensu duk da yake daga cikinsu akwai wadanda suka yi aure. yayinda kungiyar ta zargeta da cewa tana boye 'ya'yanta mata a daki, yayinda ita kuma take zama ba miji.

Ga ci gaban rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Matan Da Suka Kubuta Daga Hannun Boko Haram-2:50