Dan Kunar Bakin Wake Ya Kai Hari Kan Gidajen 'Yan Sanda A Masar.

Akwatunan gawarwakin wasu 'Yansanda da aka kashe a yankin Sinai a 2013

Wani dan harin kunar bakin wake, dake tuka wata mota da aka dankarawa nakiyoyi ya kaiwa gidajen yan sanda hari a zirin Sinai can kasar Masar da sanyin safiyar jiya Talata, ya kashe farar hula daya da raunana 'yan sanda ashirin da hudu.

Jami'an tsaro sunce yan sanda sun harbi motar, a lokacin data doshi gidajen, to amma direban motar yaki tsayawa. Harbin da yan sanda suka yi ne, ya tada bama baman, kuma tashin bama-baman ne suka kashe farar hulan.

Nan da nan babu kungiyar data yi ikirarin cewa ita keda alhakin kai harin.

To amma an sha dorawa 'yan yakin sa kai alhakin hare haren da aka sha kaiwa a zirin Sinai, hare haren da suka karu tun lokacinda shugaban kasar Abdel Fatah El Sissi, ya hambarar da gwamnatin shugaba Morsi a shekara ta dubu biyu da goma sha uku, yana matsayin hafsan sojojin kasar.

Galibi sojoji da 'yan sanda ake aunawa wajen kai hare hare

A ranar Litinin ma, wani bam da aka boye a gefen hanya ya kashe sojoji uku kusa da El Arish.