Rahotanni daga jihar Taraba arewa maso gabashin Najeriya na cewa an samu asarar rayuka masu yawa a wani sabon rikici da ya sake barkewa a garin Tella,cikin karamar hukumar Gassol,wanda kawo yanzu ba’a san adadin mutanen da aka kasha ba,yayin da wasu da dama ke asibiti ana jinyar su.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka tabbatar,baya ga rayukan da aka kashe,haka nan kuma,an kona gidaje da kuma wuraren sana’a masu dinbin yawa.
Haka nan kuma,rikicin dai ya samo asali ne bayan wani sabani da cacar bakar da ta taso a tsakanin wani matashi dan kabilar jukun,da kuma wani bahaushe a bakin kogin,kafin daga bisani lamarin ya fantsama zuwa cikin gari.
Rundunan yan sandan jihar Taraban ta bakin kakakinta ASP Joseph Kwaji ta tabbatar da wannan sabon rikicin,wanda tace kawo yanzu tana cigaba da bincike na sanin adadin rayukan da suka salwanta,wanda kuma tuni aka kama wasu da ake zargin suna da hannu a tashin hankalin.
Ba wane dai karon farko da ake samun irin wannan hatsaniya a tsakanin al’ummomin jukun da abokanan zamansu Fulani da Hausawa,wanda sau tari rikicin kan koma fadan kabilanci dana addini,wanda masana irinsu Alh.Muhamamdu Danburam na cibiyar cigaban yankunan karkara na Rural Development Initiative ke dangantawa da jahilci da kuma zukin yan ingiza mai kantu ruwa.
Your browser doesn’t support HTML5