An Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Ukraine.

Wata mace take wucewa kusa da wani gini da aka lalata a garin Vuhlehirsk kusa da Donetsk, Ukraine.

Ana zargin wasu tsararu daga Rasha a zaman wadanda suka kai harin da makaman Egwa.

A Ukraine wani jami'in kasar ya bada rahoton an keta yarjejeniyar tsagaita wuta da asubahin lahadin nan, jim kadan bayan da yarjejniyar ta fara aiki, da nufin kawo karshen fada da ake yi a gabashin kasar, tsakanin sojojin Ukraine, da 'yan aware na kasar wadanda suke samun goyon bayan Rasha.

Shugaban hukumar tsaron kasar Valentyn Nalyvaichenko, yace akwai alamun cewa wasu tsiraru daga Rasha da ake kira Cossack sune suke da alhakin kai harin da bindigogin egwa a yankin Luhansk. Yace za'a fara bincike akai.

Tunda farko Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya umarci dakarun kasar su mutunta shirin tsagaita da ya fara aiki da karfe 12 na daren jiya Asabar, watau karfe 4 na asubahi agogon Najeriya, da Nijar da kamaru, Sa'o'i bayan da aka gwabza kazamin fada a gabashin kasar.

A cikin jawabi da ya gabatar ga al'umar kasar kai tsaye ta talabijin, Mr. Poroshenko, yace a matsayinsa na kwamandan askarawan kasar, yana son ganin an cimma zaman lafiya, duk da haka ya gargadi 'yan tawayen da Rasha take daurewa gindi cewa, su guji keta yarjejeniyar.

Mr. Poroshenko yayi gargadin cewa 'yan tawayen zasu so suyi amfai da garin Debaltseve, wajen gurgunta aiki da yarjejeniyar. Garin mai tashar jiragen kasa, ya kasance wuri da aka gwabza fada mai tsanani har zuwa lokcin da 'yarjejeniyar ta fara aiki, yayinda sojojin Ukraine da 'yan tawayen suka yiwa zobe a garin, suka ja daga.

Shugaban 'yan tawaye daga birnin Donetsk, yace mayakansa ba zasu kyale sojojin Ukraine su fice daga garin ba a lokacin da ake mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar.

A karkashin jarjejeniyar da turai ta shiga tsakani aka kulla a birnin Minsk, sojojn Ukraine, da 'yan tawaye wadanda Rasha ta daurewa gindi, zasu tsaida fada. Idan hakan ya dore, duka sassan biyu zasu fara janye manyan kayan yakinsu baya, domin a girke a wuri da za'a kira tudun mun tsira.