Da dage zaben Najeriya zuwa karshen watan Maris, duka manayn jam'iyun siyasar kasar, PDP da APC suka ce a shirye suke, suna kwada kansu cewa, ko yanzu aka yi zabe to jam'iyyarsu ce zata sami nasara.
Mukaddashin darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan Alhaji Isa Tafida Mafindi yace yakin neman zabe tamkar yaki ne ko wace jam'iyya tana da nata hikima na yadda zata tallata kanta ta zamanto ta karbu ga jam'a musamman wadanda sabbi ne a harkar zabe da kuma tsoffin hanu.
Tafida, yace ba kamar APC ba, su ba hayana mutane suke yi daga ko ina zuwa wasu wurare domin kawai a ce ai suna da mutane. Yace abunda zai sa PDP ta sami nasara shine irin ayyuka da wannan gwamnati tayi a fannin sifirin jiragwen sama dana ruwa, da kuma na kasa. Da kuma aikin noma.
Amma a nata bangaren mukaddashiyar darektar yada labarai ta jam'iyyar APC Hajiya Naja'atu Mohammed, da farko ta karyata irin ayuka da gwanatin PDP take ikirarin ace tayi.
Tace, babban aikin gwamnatin tarayya shine kare rayuka da dukiyar al'uma, wanda ko wani da Najeriya zai shaida ta gaza a wannan fanni.
Ga rahoto
Your browser doesn’t support HTML5