A Pakistan, hukumomin kasar suka ce an kashe akalla mutane 58 wasu fiyeda hamsin kuma sun jikkata sakamakon fashewar wani bam mai karfi a masallacin 'yan shi'a marasa rinjaye a lardin Sindh, lokacin ana sallar jumma'a.
An kai harin ne a yankin da ake kira Lakidar na Shikarpur, mai tazarar kilomita 470 arewa da birnin karachi mai tashar jiragen ruwa.
Da yawa daga cikin wadanda suka jikkata an bada labarin suna cikin mawuyacin hali.
Wata kungiyar da ake kira Jundallah, wacce ta balle daga kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wannan hari, na baya bayan nan a karuwar tarzomar kan sabanin akida a Pakistan.
'Mabiya mazhabar sunni masu tsatstsaurar ra'ayi galibi suna auna hare hare kan cibiyoyin 'yan shi'a wadanda yawansu yakai kashi daya cikin biyar na al'umar kasar.
Babban sakataren MDD Ban ki-moon, yace ya kadu ainun, kan irin wannan tsagwaran mugunta ta kaiwa mutane hari saboda banbancin akida".Daga nan yayi kira ga hukumomin Pakistan su kara zake dantse a kokarinsu na kare tsiraru ta fuskar addini ko kabila.
An kashe mabiya darikar shi'a fiye da dari takwas a Pakisyan cikin shekaru biyu da suka wuce.
Kasar tana cikin shirin ko ta kwana tun cikin watan Disemba bayan da mayakan Taliban suka kai hari kan wata makarantar a Peshwar da ya halaka mutum dari da arba'in da biyar, galibinsu yara.