Amurka Ta Gurfanar Da Wasu Mutane Kan Juyin Mulki Da Bai Sami Nasara Ba A Gambiya.

Yahya Jammeh da uwargidansa Zineb Jammeh, a fadar white House bara.

Daya daga cikin mutanen ya amsa laifin makarkashiyar juyin mulkin.

Lauyoyin gwamnatin Amurka sun tuhumi mutum na uku ba Amurke, a gaban shari'a dangane yunkurin juyin mulki da aka so yi a Gambia cikin watan jiya.
Jiya jumma'a ma'aikatar shari'a tace an gabatar da tuhuma kan Alagie Barrow da shekaru 41 da haifuwa a gaban wata kotun Amurka a Minnesota, kan zargin hada bakai da kulla makarkashiya na kai hari kan wata kasar da Amurka bata gaba da ita. Da kuma zargin karya dokoki kan mallkar makamai. Wanda ake zargin Barrow yana da zama ne a jihar Tennessee, kuma dan kasashen duka biyu ne Amurka da Gambia.
A ranar Alhamis wani ba Amurka ya amsa laifi kan zargi mai nasaba da juyin mulkin. Papa Faal dan shekaru 46 da haifuwa, ya amsa a gaban kotu cewa yana cikin wadanda suka kai hari kan fadar shugaban kasar Gambia ranar 30 ga watan Disemba a babban birnin kasar Banjul.
An tuhumeshi ne da laifin hada baki don jigilar makamai zuwa Gambia, da kuma makarkashiyar kifar da gwamnati wata kasar ketare da take zaman lumana da Amurka. Shima Fa'al dan Gambia haka kuma ba Amurke ne.
Hukumomin Amurkan tun da farko sun kama wani dan kasar dan kasuwa a jihar Texas mai suna Cherno Njie. Ma'aikatar shari'a tace wadanda suka shirya juyin mulkin sun yi fatar nada dan kasuwar Njie a matsayin shugaban kasar na wucin gadi.
Fa'al ya gayawa hukumomi cewa su da suka shirya juyin mulkin sunso ne su kai hari kan jerin gwanon motocin shugaban kasar, amma sai suka sake shawara da suka sami labarin cewa shugaba Yahya Jammeh baya kasar.
Masu tsaron fadar shugaban kasar suka tarwatsa harin. Fa'al yace "sunyi mamakin turjiyar da suka samu, da basu tsammaninta ba."