Mali Ko Guinea? Ana Shirin Yin 'Yar Tinke Yanzun Nan

Nan da wani dan kankanin lokaci za a san kowace kasa ce zata haye zuwa wasannin kwata-fainal a matsayin ta biyu a rukunin D tsakanin Mali da Guinea, bayan da aka kammala wasannin rukunoni kasashen biyu su na canjaras.

Kamar yadda aka yi tanadi a sashe na 74 na dokokin Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ya tanada, za a gudanar da zaben mai-rabo-ka-samu domin tantance kungiyar da zata zo ta biyu a rukun in D a tsakanin Mali da Guinea.

Za a gudanar da wannan zaben a lokacin taron da za a yin a Kwamitin Shirya Gasar Cin Kofin kasashen Afirka yau alhamis da karfe 4 agogon Equatorial Guinea a hotel din Hilton na Malabo.

Za a saka kwallaye guda biyu a cikin wani Kwando, daya an rubuta lamba 2 a jiki, dayan kuma an rubuta lamba 3 a jiki. KOwace kasa zata sanya wakilinta ya dauko kwallo guda, sai a duba jiki. Duk kasar da ta dauki wanda aka rubuta lamba 2 a jiki, to zata haye zuwa wasannin kwata fainal, wadda ta dauki lamba ta 3 kuma, zata koma gida.