Masu kula da harkokin saye-da sayarwar kasar China sun zargi kamfanin Alibaba da bari a saida kayayyakin jabu da kuma barin ‘yan kasuwa shiga harkokin kasuwanci ba tare da lasi ba, bisa ga wani rahoto da aka bada a shekarar da ta gabata amma ba a fidda shi ba sai yanzu, watanni 6 bayan da kamfanin ya fara saida hannun jari a birnin New York.
Ba a cika samun irin wannan tsautawar da aka yi yau laraba ba daga gwamnatin China, musamman ganin irin mutuncin Alibaba a matsayin mai saida kayayyaki ta hanyar yanar gizo mafi girma da ake kyautata zaton shi ke da fiye da rabin harkar tsarin kasuwancin kai tsaye tsakanin mai sarrafawa da mai saye.
Tayi na farko da kamfanin Alibaba yayi na hanunn jarin birnin New York ya kai dala biliyan 25 a watan Yulin shekarar da ta gabata.
Hukumar da ta gabatar da sanarwar, wato hukumar kula da harkokin masana’antu da kasuwancin china , ta fadi cewa, kamfanin Alibaba ya bada damar saba dokokin saye-da-sayarwa ta hanyar yanar gizo har na tsawon lokaci. Bugu da kari akan masu saida kayan da basu da lasi da kuma saida jabun kayayyaki, Cibiyar ta zargi Alibaba da nuna tallar bogi.
Kammfanin Alibaba ya maida wa Cibiyar murtani, inda ya zarge ta rashin bin ka’ida.
Rahoton dai da martanin da kamfanin Alibaba ya bada sun zo ne ana gobe kamfanin zai fidda sakamakon cinikinsa na kwata-kwata da yake fidda wa.
Your browser doesn’t support HTML5