David De Gea Na Iya Barin Manchester United In Ji Manajansa

David de Gea, mai tsaron gidan Manchester United

Duk da cewa sai a shekara mai zuwa ne kwantarakin mai tsaron gidan Manchester United, David de Gea, zai kare, wakilinsa Jorge Mendes, yace tana yiwuwa ya canja sheka kafin nan.

Mendes, wanda sauran ‘yan wasan da yake wakilta ko zaman musu agent sun hada da Cristiano Ronaldo da Radamel Falcao, yace lamarin yana sauyawa kusan a bayan kowasu ‘yan mintoci.

A bana dai, de Gea dan kasar Spain, yana burgewa sosai wajen tsaron gida ma ‘yan Red Devils din, amma kuma har yanzu shugabannin kungiyar ba su gabatar masa da tayin sabon kwantaraki ba, duk da cewa wannan ita ce shekarar karshe a kwantarakin nasa.

Kungiyoyin dake zawarcin de Gea sun hada har da Real Madrid wadda take neman magajin mai tsaron gidanta Casillias, yayin da Manchester United ta yi sauri ta sayi wani tsohon hannu wajen tsaron gida, Victor Valdes, ko da shi de Gea mai shekaru 24 zai nemi sauya sheka.

A yanzu wakilin nasa, Mendes ya kara rura wutar jita jitar cewa de Gea zai bar Manchester United, kamar yadda ya janye Ronaldo daga Man U din zuwa Madrid, a lokacin da ya furta cewa “David dai gawurtaccen dan wasa ne. Shi dan Manchester United ne don yana da kwantaraki a can. Dole a mutunta hakan, amma kuma, komai na iya canjawa cikin minti biyar tak.”

Manajan Man U dai, Louis Van Gaal, yace David de Gea zai kara wa’adin kwantarakinsa a kulob din, a bayan da ya kara jaddada matsayinsa na mai tsaron gida na 1.