Gidan telebijin na Saudi Arabiya ya bada sanarwar rasuwar Sarki Abdullahi bin Abdul'aziz al-Sa'ud a cikin daren nan.
An nada kaninsa Salman bin Abdul'aziz al-Sa'ud a zaman sabon Sarki.
Sabon sarki Salman kuma yayi kira ga Majalisar Mubayi'a da ta kunshi iyalan gidan sarautar al-Sa'ud da su yi mubayi'a ga kaninsa MUqrin a zaman Yarima mai jiran gado kuma magajinsa.
Sanarwar da gidan telebijin din ta yada ta ce, "Mai Martaba Salman bin Abdul'aziz al-Sa'ud da dukkan iyalan gidan sarauta da kuma al'ummar Sa'udiyya su na jimamin rashin Mai Rikon Masallatai Biyu Masu Tsarki, Sarki Abdullahi bin Abdul'aziz, wanda ya rasu da karfe 1 na daren nan."
Sarki Abdullahi, wanda ake tsammanin an haife shi a 1923, ya zamo Sarkin Sa'udiyya a shekarar 2006 a b ayan rasuwar yayansa Sarki Fahd.
Sabon Sarkin Sa'udiyya, Salman, wanda ake tsammanin shekarunsa na haihuwa 79 ne, ya zamo Yarima mai jiran gado a 2012. Kafin nan yayi shekaru 50 yana gwamnan lardin Riyadh.
A cikin wata sanarwa daga fadar White House, shugaba Barack Obama na Amurka ya mika sakon ta'aziyyarsa da kuma jimamin Amurkawa ga iyalan marigayi Sarki Abdullahi da al'ummar Saudi Arabiya.