A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka da ake yi a kasar Equatorial Guinea, a yau laraba Gabon zata kara da Kwango, yayin da take ci gaba da more matsayinta na daya a rukunin farko ko A, bayan da ta doke Burkina Faso da ci 2 da babu a wasansu na farko ranar asabar.
Kafin wannan wasan kuwa, ita Burkina Faso zata kece raini da mai masaukin baki Equatorial Guinea, a yayin da ‘yan Burkina din ake sa ran zasu mike tsaye domin in har suka sha kashi yau, to watakila tun a zagayen farko zasu koma gida, don har yanzu basu samu koda maki daya ba.
Equatorial Guiena da Kwango dai suna da maki daya daya a bayan kunnen dokin da suka yi ran asabar.
JIya talata, an tashi kunnen doki a dukkan wasannin da aka buga da ci daya da daya, inda Cote D’Ivoire da Guinea suka yi daya da daya a wasan da aka kori dan wasan CI Gervinho daga fili, kuma zakaran kwallon kafa na Afirka Yaya Toure ya kasa nuna bajimta.
Mali da Kamaru ma sun tashi babu kare bin damo da ci daya da daya.