Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sayi dan wasa Wilfried Bony dan kasar Ivory Coast daga kungiyar kwallon kafa ta Swansea City kan kudin da ba a bayyana ba.
Sai dai an ji cewa City, wadda it ace ke rike da kambin Firimiya Lig, ta cimma daidaituwar fam miliyan 27 da kungiyar Swansea, kuma zata rika biyan Bony albashin fam dubu 75 a kowane sati.
Raunin da Sergio Aguero ya ji, wanda shine ya fi jefa ma City kwallaye a raga, da kuma rashin kuzarin ‘yan wasanta irinsu Edin Dzeko da Stevan Jovetic, sun sa ala tilas Manuel Pellegrini, manajan City, yana sanya James Milner a can gaba, amma kuma kungiyar ta yi gaggawa ta sayi dan wasan da take jin cewa zai karfafa ‘yan wasanta na gaba.
Bony, wanda watakila ba zai koma City ba sai tsakiyar Fabrairu idan har Ivory Coast ta kai wasan karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka da za a fara a karshen mako. A yanzu kungiyar Manchester City tana da dukkan ‘yan wasa guda uku da sune a hade suka fi yawan kwallaye a shekarar da ta shige, watau Bony, Aguero da kuma Yaya Toure.