A shekarar 2014 da ta gabata, shahararrun masu fina-finan barkwanci na Hausa da dama sun rasu, cikinsu har da Rabilu Musan Danlasan, watau Ibro, da Shehu Golobo.
Ita dai wannan masana'anta ta fina-finan Hausa da ake kira Kannywood, ta yi rashin Rabilu Musa Dan Ibro dab da karshen shekarar, watau a ranar 10 Disamba, 2014, bayan ya jima yana fama da rashin lafiya. Marigayi Ibro, ya rasu a Kano, bayan ya komo daga wata jinyar a kasar Indiya.
Shi kuwa fitaccen jarumin fina-finan barkwanci Shehu Golobo, ya rasu a ranar Alhamis 30 ga Janairu, 2014 a Sakkwato.
Ko a bayansu kuma, akwai wasu fitattu a wannan harkar fina-finan Hausa da suka rasu a shekarar ta 2014, cikinsu har da Musa Jalingo, a ranar Alhamis 15 ga Mayu, 2014 a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano; da Faruk Nagudu mai kamfanin Nagudu Investment a ranar Asabar 14 ga Yuni, 2014 shi ma a Asibitin Malam Aminu Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya.
A watan Nuwamba ne Abubakar Buwa wanda ake yi wa lakabin Darakta, wanda ke harkokin wasan kwaikwayo a Jabi daki-Biyu da ke Abuja ya rasu a Kano bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Wasu sanannun 'yan fim din kuma sun yi rashin iyayensu, cikinsu har da Samira Saje da kuma Aminu Almah na Jos.