Wani Kamfanin Rasha Yace Zai Iya Gina Sansanin Bincike A Kan Wata

Neil Armstrobng, bil Adama na farko da ya fara taka wata, yana ciro kaya daga kan kumbon da ya sauka da su doron Wata. Buzz Aldrin shi ne ya dauki wannan hoton.

Wani kamfanin kasar Rasha ya bada sanarwar cewa zai iya gina wani sabon sansanin bincike na dindindin a kan Wata, wanda kuma zai ci kudi dala miliyan dubu tara da dari uku.

Kamfanin mai suna Lin Industrial, ya zana sabon sansanin wanda yace za a gina a dab da wani dutse mai suna Malapert Mountain a kusa da kuryar kudancin Wata, wanda kuma za a gina shi daki-daki har biyu.

A matakin farko, sansanin zai iya daukar ma'aikata biyu, amma idan aka kammala shi, mutane 4 zasu rika zama a cikinsa.

Tsare-tsaren kamfanin a yanzu sun nuna cewa za a harba rokoki har 37 dauke da kayan aiki kafin a iya kammala aikin gina wannan sansani akan wata, ciki har da rokoki 13 da zasu tafi da kaya mai nauyi.

Kamfanin yace jigilar kaya da gine-ginen farko zasu dauki shekaru biyar, kuma za kammala dukkan aikin ginin sansanin cikin shekaru 10.

Ba a dai san ko kamfanin ya samu kudin gudanar da wannan aikin, ko kuma yadda zai fara shi ba. Amma ganin cewa akwai wasu kamfanoni da kasashen dake shirye-shiryen gudanar da wasu ayyuka a kan Wata, wannan alama ce ta sabuwar sha'awar ci gaba da binciken abu mafi kusa da duniyar bil Adama a wannan bangare na falaki.